KANFEST 2025: Gwamna Abba ya umarci sarakunan Kano da su ci gaba da hawan sallah

Date:

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci dukkanin Sarakunan jihar da su ci gaba da gudanar da bikin hawan sallah a kowacce shekara, domin tabbatar da ci gaba da adanawa da kuma yada al’adun gargajiya na Jihar .

Gwamna Yusuf ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta ba da cikakken goyon baya ga masarautu domin tabbatar da cewa wannan tsohuwar al’ada ta ɗore, ta ƙara ƙarfi, kuma a nuna ta ga duniya baki ɗaya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a wajen bude taron KANFEST (Kalankuwa) 2025, wanda aka shirya domin nuna ɗimbin al’adun Kano da ƙarfafa masu fasaha, da haɗa kan matasa da mata tare da gina haɗin gwiwa ta duniya wacce za ta ɗora Kano a taswirar al’adu ta duniya.

A nasa jawabin, Sarkin Kano na 16 kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, Dr. Muhammadu Sanusi II, ya yabawa hangen nesa na Gwamnatin Jihar Kano wajen dawo da girmamawa ga al’adun mutanen Kano waɗanda suka taɓa dusashewa.

Wannan biki na kwanaki uku zai ƙunshi nunin al’adu da abincin gargajiya da wasan kwaikwayo da wasanni, da kayan ɗinki da tukwane da gabatar da makalu daga masana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...