Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da yajin aikin gargadi na makonni biyu da ta fara a makon da ya gabata a dukkan jami’o’in gwamnati a faɗin ƙasar.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a babban ofishin ASUU da ke Abuja a ranar Laraba.
Farfesa Piwuna ya bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bayan shiga tsakani daga Majalisar Dattawa tare da wasu masu ruwa da tsaki, domin samar da fahimtar juna tsakanin gwamnati da ƙungiyar.
Sai dai ya ƙara da cewa, Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (NEC) ta ASUU ta ba wa gwamnatin wa’adin wata guda domin magance matsalolin da suka haddasa yajin aikin, inda ya yi gargadin cewa ƙungiyar za ta ɗauki mataki mafi tsanani idan aka kasa cika alkawura.