Hadimin Gwamnan Kano yasa yansanda sun tsare ɗan jarida a Kano

Date:

Wani ɗan jarida a jihar Kano, Ibrahim Dan’uwa Rano, ya shiga hannun ƴansandan Hedikwatar Rundunar Ƴansanda ta Shiyyar Kano bayan Darakta Janar na ofishin tsare-tsaren na gidan gwamnati, Abdullahi Rogo, ya shigar da ƙorafi yana zargin ɗan jaridar da ɓata masa suna.

Rogo na fuskantar bincike daga EFCC da ICPC kan zargin badakalar naira biliyan 6.5.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƴansanda sun cafke ɗan jaridar ne a ofishinsa ya na tsaka da aiki, ba tare da nuna masa takardar umarnin kame ba, sannan su ka garzaya da shi zuwa hedikwatar ƴansanda ta shiyya ɗaya domin yi masa tambayoyi.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana tuhumar Rano da laifin ɓata suna da kuma gudanar da tashar talabijin ta yanar gizo ba tare da samun lasisi daga Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC) ba.

A cikin wani shiri da ya ke gabatarwa, mai suna “Imalu”, Dan’uwa Rano ya yi wani habaici, inda ya ce “wani shugaban ofishin tsare-tsare yana karɓar cin hanci kafin baiwa baƙi damar ganawa da ubangidansa.”

Ko da yake bai ambaci sunan DG Rogo ko na gwamnan a cikin shirin ba, ƴansanda sun nace cewa sai ya baiyana ma’anar “Imalu”.

Sai dai Daily Nigerian ta ce rundunar ƴansanda, shiyyar Kano ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da kama da kuma tsare ɗan jaridar har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...

RMK@69: Kwankwaso Jagora Ne Mai Hangen Nesa, Abba Kuma Na Kawo Ci Gaba a Kano – Bakwana

Wani jigo a kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon mai ba...