Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Date:

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen jihar Kano ta bayyana mamakinta kan kalaman da ake cewa mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi game da ma’aikatan jinya da unguwar zoma.

Idan za a iya tunawa mataimakin gwamnan ya bayyana cewa ma’aikatan jinya da Ungozoma sun Gaza wajen gudanar da aikinsu yadda ya dace.

Mukaddashin sakataren kungiyar a jihar, Kwamared Nas Ahmad Hamzat Sharada, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar kungiyar da ke Kano.

Kwamared Sharada ya ce kalaman da mataimakin gwamnan ya furta sun yi matuƙar girgiza su, duba da irin rawar da ma’aikatan jinya da unguwar zoma ke takawa wajen ceton rayukan al’umma a asibitoci daban-daban.

“Ma’aikatan jinya da ungozoma suna aiki ba dare ba rana wajen kula da marasa lafiya, musamman mata masu juna biyu da jarirai. A gaskiya su ne ke aiwatar da kusan kashi 75 cikin 100 na ayyukan da ake yi a asibitoci,” in ji Sharada.

Ya ƙara da cewa bai dace da matsayin mataimakin gwamna ba ya fito yana furta kalaman da ka iya rage kimar ma’aikatan da ke aiki tukuru wajen tabbatar da lafiyar jama’a.

“Yakamata mai girma mataimakin gwamna ya yi nazari kafin ya yi irin waɗannan kalamai. Ma’aikatan jinya da unguwar zoma suna bin doka da ƙa’idojin aiki, kuma suna ba da gudummuwa wajen cigaban jihar,” in ji shi.

A nasa jawabin, sakataren kuɗi na ƙungiyar a jihar, Kwamared Yahaya Shehu Muhammad, ya ce “Idan Allah ya ba mutum lafiya, wata rana zai iya zama gwamna. Saboda haka bai dace kalamai masu nuna raini su rinka fitowa daga bakin manyan jami’an gwamnati ba.”

Kungiyar ta bukaci gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba batun tare da ƙarfafa ma’aikatan jinya da unguwar zoma don su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin kwarin gwiwa.

An yi ƙoƙarin jin ta bakin sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, amma har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, ba a samu amsa daga gare shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...