Gwamnatin jihar Kano ta kai tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ‘ya’yansa biyu da wasu mutum shida kotu bisa zargin yin almundahanar kudi naira biliyan 4.49.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa an shigar da karar ne a babbar kotun jihar Kano a ranar 13 ga Oktoba, 2025, inda gwamnati ke neman a maido da kashi 20 cikin 100 na kudaden da aka zuba a Dala Inland Dry Port Limited, da kuma dawo da kudin da ake zargin an karkatar.

Wadanda ake tuhuma sun hada da Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ‘ya’yansa Umar da Muhammad, tsohon mai ba shi shawara Abubakar Sahabo Bawuro, tsohon sakataren hukumar Nigerian Shippers Council Hassan Bello, lauya Adamu Aliyu Sanda, da kamfanin Dala Inland Dry Port Limited.
A cewar takardar tuhumar, ana zargin wadanda ake tuhumar da laifuka goma da suka hada da hada baki wajen karkatar da kudaden al’umma, cin amana da kuma sabawa doka.