Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya Lokacin Zaɓen Shugaban Ƙasa Da Na Gwamnoni Zuwa Nuwamba, 2026
An gabatar da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ta 2025 (Electoral Act Amendment Bill 2025) a yayin zaman sauraron ra’ayoyin jama’a da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, wanda Kwamitocin Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai kan Harkokin Zaɓe suka shirya tare.
A cikin kudirin, majalisar ta ba da shawarar a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnonin jihohi a watan Nuwamba, 2026, wato watanni shida kafin lokacin da ake gudanar da irin wannan zaɓe a da.
Kudirin ya tanadi cewa, “Zaɓen ofishin shugaban ƙasa da na gwamnan jiha dole ne a gudanar da shi ba fiye da kwanaki 185 kafin karewar wa’adin mai rike da mukamin a yanzu.”
Wannan sabon tsarin zai sa zaɓukan gaba na ƙasa da jihohi su gudana a Nuwamba, shekarar 2026.