Taron Zuba Jari na Bauchi: Sabuwar Damar Bunƙasar Tattalin Arziki – Daga Lawal Muazu Bauchi

Date:

 

Ga dukkan alamu, Jihar Bauchi na fitowa a hankali a matsayin abin koyi wajen mulki nagari da zuba jari mai ma’ana a Najeriya. Taron tattalin arziki da zuba jari da aka kammala kwanan nan a jihar Bauchi ya kara tabbatar da wannan ci gaba, inda ya zama wani tarihi a ci gaban tattalin arzikin jihar da makomar ta.

An kammala wannan taro, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin jihar, da kyakkyawan sakamako inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna guda 47 (MoUs) a bangarori masu muhimmanci kamar noma, ma’adanai, wutar lantarki, yawon bude ido da masana’antun hakar albarkatu. Jimillar darajar jarin da aka samu ya kai sama da Dala biliyan 5.2 (kimanin Naira tiriliyan 7.8). Wannan matakin ya nuna yadda masu zuba jari ke kara yarda da yanayin tattalin arziki na Bauchi, hanyoyin manufofi, da kwanciyar hankali a shugabanci.

Daya daga cikin manyan yarjejeniyoyin da aka cimma ita ce ta Dala biliyan 2.7 da Kamfanin China Fuhai Energy Group don gina babban birnin masana’antar sinadarai (Petrochemical City Complex) a Bauchi. Haka kuma, akwai zuba jari na Dala biliyan 1 daga African Athlete Academy don kafa cibiyar bunkasa wasanni da matasa ta zamani, da nufin kula da hazaka da inganta rawar matasa. Wadannan yarjejeniyoyi sun bude sabon babi ga jihar Bauchi, inda suka mayar da ita cibiyar masana’antu da bunkasar dan Adam.

A bayan wadannan nasarori akwai wani shugaba mai hangen nesa wanda ya sadaukar da kansa wajen sauya jihar Bauchi zuwa jiha mai ci gaba da dorewa. Tun da ya hau mulki a shekarar 2019, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya nuna cewa shugabanci ba wai iko ba ne kawai, ya ƙunshi hangen nesa, hadin kai da samar da sakamako mai kyau. Gwamnatinsa ta fifita tasiri na dogon lokaci fiye da kwalliya da za a riƙa gani ta waje, inda take samar da ababen more rayuwa da za su amfani al’umma kai tsaye.

Aiki tare da Gwamna Mohammed ya bani cikakkiyar ƙwarewa da fahimtar yadda shugabanci nagari ke kasancewa. Shugaba ne mai saukin kai, kuma yana matukar kishin al’umma, kuma yana da jajircewa wajen aiwatar da manufofin da ke inganta rayuwar al’umma. Yana sauraron shawara, yana daraja aiki tare da girmama kowa a cikin ma’aikatan sa. Wannan yanayi na yarda da juna da bada damar tattaunawa ya sa tawagarsa ke aiki cikin hadin kai da nasara.

Daya daga cikin bangarorin da su ka fi daukar hankali a karkashin mulkinsa shi ne ci gaban ababen more rayuwa. Hanyoyin da aka manta da su da suka zama marasa amfani an sake gina su, gini na zamani, wanda ya inganta da saukaka zirga-zirga a fadin jihar. Hanyar Ibrahim Bako Bypass (wanda ake kira Gombe–Maiduguri Bypass) da Sabon Kaura–Miri Road su ne misalai na ayyukan da suka sauya harkokin sufuri, inganta ci gaban tattalin arziki da karfafa hadin kan al’umma. Wadannan ci gaba na canza fasalin jihar Bauchi da dawo da amana tsakanin gwamnati da jama’a.

Hangen nesa na Gwamna Mohammed game da mulki da maida hankali kan hidimar al’umma ya bayyana a bangaren ilimi da lafiya. Bangaren ilimi ya samu sauye-sauye sosai, inda aka gyara makarantu da dama ko kuma aka gina sababbi tare da kayan aiki na zamani. Gwamnatinsa ta dauki malamai kwararru tare da horas da su don tabbatar da cewa kowane yaro a Bauchi yana samun ingantaccen ilimi.

A bangaren lafiya kuwa, Gwamna Mohammed ya ayyana dokar ta baci don magance matsalolin da aka dade ana fuskanta. An gyara cibiyoyin lafiya tare da karfafa bayar da kula da lafiya a matakin farko, musamman a kauyuka. Wadannan matakan sun kara samuwa da amfani da ayyukan jinya da kuma inganta lafiyar al’umma gaba daya.

Bangaren noma, wanda shi ne ginshikin tattalin arzikin Bauchi, ya samu kulawa fiye da kowane lokaci. Ta hanyar samar da iri ingantattu, taki da kayan aikin noma na zamani, gwamnati tana taimaka wa manoma su koma daga noman gargajiya zuwa noman kasuwanci. Tare da hadin gwiwa da kungiyoyi kamar CSC Farms, dubban matasa na samun horo a sabbin hanyoyin noma, suna zama manoma zamani da ke taimakawa wajen samar da abinci da habaka tattalin arziki.

Dabarun mulki na Gwamna Mohammed na tafiya daifai da muradun al’umma na daga cikin abin da ke nuna kwazonsa. Ya na ziyarar aiki akai-akai domin tabbatar da inganci da saurin aiki. Hakanan ya na bude kofa ga jama’a sannan ya saurari bukatu da ra’ayoyinsu. Wannan tsarin na shugabanci da ya dogara da al’umma ya sa gwamnatin Bauchi ta zama mai gaskiya, amintacciya da kusanci da al’umma.

A gare mu da mu ke aiki da shi, Gwamna Mohammed ba shugaba ba ne kawai, shi uban gida ne da ke karfafa mana gwiwa. Ya na daraja gaskiya, aiki tukuru da aminci. Ya na kula da ma’aikatansa kamar iyalansa, kuma kullum yana tuna mana cewa shugabanci hidima ne, ba jin daɗi ba. Wannan dabi’a ta tawali’u da gaskiya ta sa ya samu girmamawa daga abokan aiki, jama’a da kungiyoyin ci gaba.

Nasarar Taron Zuba Jari na Bauchi ba kawai nasara ce ta tattalin arziki ba. Alamar sabon zamani ne na farfadowar al’amurra, ci gaba da gina sabuwar Bauchi. Wata shaida ce da ke nuna cewa Bauchi ta shirya don daukar matsayinta na gaskiya a cikin tattalin arzikin kasa da duniya. Hakanan yana karfafa kudurin Gwamna Mohammed na gina tattalin arzikin da ke dogaro da kansa, wanda ya dogara da kirkire-kirkire, jarin masu zaman kansu da hadin kan al’umma.

A matsayina na wanda Allah ya ba dama in kasance cikin wannan gwamnati, zan iya tabbatar da cewa ginshikan da ake dasa yau za su tsara makomar Bauchi har zuwa shekaru masu zuwa. Labarin Bauchi a karkashin shugabancin Gwamna Mohammed labari ne na sauyi, wanda aka gina bisa jarumta, hangen nesa da jin kai. Gudu ba ja da baya, ci gaban yana bayyane, hangen gaba kuma a fili yake. Jihar Bauchi a bude take ga kasuwanci, hadin gwiwa da kuma makomar ci gaba. A karkashin jagorancin Gwamna Mohammed, alkawarin samun Bauchi daya, mai gaba da kuma mai wadata yana zama gaskiya.

Lawal Muazu Bauchi
Mai Taimaka wa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed kan Harkokin Sadarwa ta Intanet
Ya rubuto daga Karofi, Bauchi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...

Da dumi-dumi: ASUU ta sanar da ranar da zata fara yajin aiki

Shugabancin Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci...

Kananan Hukumomin Tarauni Rogo da Doguwa sun zamo koma baya wajen yin rijistar Masu zabe a Kano

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu kananan hukumomin...

Jami’an Civil defence sun kama dilan wiwi a Kano

Rundunar tsaron farar hula (NSCDC) a jihar Kano ta...