Yan sanda a Kano sun ceto mutane 2 da aka yi garkuwa da su tare da kwato kayiyyaki

Date:

Rundunar ‘yan Sanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce ta sami nasarar ceto wasu mutane biyu da masu garkuwa suka sace, tare da kwato wasu muhimman kayayyakin a wajensu a yayin wasu ayyukan bincike daban-daban da aka gudanar.

Haka na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24.

Ya ce rundunar ta nuna kudirin ‘yan sanda na yaki da aikata laifukan sace mutane da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

Sanarwar ta ce A ranar 7 ga Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, tawagar Anti-Kidnapping Squad tare da Surveillance Team daga ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Bebeji, sun gudanar da wani samame bayan samun sahihin bayanan sirri kan wani wanda ya kubuta daga hannun masu garkuwa.

Wanda ya kubutan, Abdul Hamid Bello, matashi mai shekaru 21, ya bayyana cewa bayan sace shi masu garkuwa da mutanen sun kuma rika dukansa, amma daga bisani ya samu damar tserewa, inda daga baya ya jagoranci jami’an tsaro zuwa sansanin masu garkuwa da mutanen da ke Saya-Saya, karamar hukumar Ikara a Jihar Kaduna.

A wajen, ‘yan sanda sun samu nasarar ceto wani dattijo mai suna Musa Idris, mai shekaru 65, yayin da masu garkuwar suka tsere bayan sun fahimci zuwan jami’an tsaro maboyar ta su. An kwato babur guda da igiya daga wajen a matsayin hujja. Daga nan aka mika wadanda aka ceto ga iyalansu domin kula da lafiyarsu.

Haka kuma, a wani samame na dabam, a ranar 9 ga Oktoba, 2025, tawagar Anti-Kidnapping Squad ta rundunar ta samu nasarar ceto wani matashi mai suna Ashiru Murtala, dan shekara 19, wanda aka sace a Beli Village, karamar hukumar Rogo, Kano, a ranar 5 ga Oktoba, 2025.

An gano cewa masu garkuwar sun ajiye shi a gonar rake da ke Hunkuyi, karamar hukumar Kudan, Jihar Kaduna, inda jami’an ‘yan sanda suka samu nasarar kubutar da shi.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya bayar da umarnin a bai wa dukkan wadanda aka ceto cikakken kulawar lafiya, tare da tabbatar da cewa rundunar tana ci gaba da gudanar da bincike don kamo wadanda suka aikata laifin. Ya kuma jaddada cewa “ba inda masu aikata laifi za su tsere a Kano.”

Rundunar ta yaba da jajircewar jami’anta da suka gudanar da wadannan ayyuka, tare da gode wa jama’ar Kano bisa hadin kai da bayar da bayanai masu amfani.

A karshe, rundunar ta shawarci al’umma da su ci gaba da lura da tsaron kansu, tare da sanar da duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba zuwa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...