Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Date:

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince da Naira miliyan 8.2 a matsayin kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026.

Daraktan Hukumar, Lamin Danbappa, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Sulaiman Dederi, ya fitar a Kano.

Danbappa ya bayyana cewa kuɗin sun yi daidai da umarnin Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) kuma sun shafi dukkan masu niyyar zuwa aikin hajji.

Ya ce masu niyyar zuwa aikin hajji da suka riga suka ajiye Naira miliyan 8.5 za a mayar musu da ragowar kuɗin bayan sun rubuta takardar neman a maida musu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, masu niyyar zuwa aikin hajji da za su fara biyan kuɗi yanzu ana sa ran su biya Naira miliyan 8.2 bisa ga umarnin da aka amince da shi.

Danbappa ya ƙara da cewa, ranar ƙarshe ta biyan kuɗin ita ce 31 ga Disamba, 2025, inda ya shawarci masu niyyar zuwa aikin hajji da su kammala biyan kuɗaɗen kafin lokacin domin tabbatar da gurbin tafiyarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...

Gwamnan Kano ya tura sunayen mutane biyu majalisar dokokin don nada su a mukaman Kwamishinoni

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika...

NLC Reshen Kebbi Ta Soki Cire Naira Miliyan 14 Daga Albashin Malamai

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta...

Ziyarar Aiki: Shugaba Tinubu Ya Iso Lagos

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Lagos...