Tsahon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta labarin da ake yadawa cewa ya rubutawa jam’iyyar APC bukatar shiga cikin Jam’iyyar.
A jiya alhamis ne dai aka ta yada labarin wanda har aka ce shi ne dalilin da yasa masu ruwa da tsakin jam’iyyar APC na jihar Kano sun gudanar da wani taron gaggawa a Abuja .
A wata sanarwa da Kwankwaso ya fitar da Safiyar Wannan rana ta juma’a ya ce labarai ba shi da tushe ballantana makama
Yace “An wayi gari da jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa mun gabatar da takardar nuna sha’awar shiga wata jam’iyyar siyasa a kasar nan.
Kwankwaso ya fito fili ya nesanta kansa daga wannan batu, inda ya bayyana cewa ba su taba mika irin wannan takarda ga kowacce jam’iyya ba.
A cikin sanarwar Jagoran jam’iyyar NNPP na Kasa ya ce yana shawartar jama’a da su ci gaba da bibiyar sahihan hanyoyin da aka tanada na ofishinsa domin samun ingantattun bayanai game da lamuransa.