Sababbin Malamai na Karamar Hukumar Garun Mallam Sun Sha Rantsuwar kama aiki

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

 

Shugaban karamar hukumar Garun Mallam, Barista Aminu Salisu Kadawa, ya yi kira ga sababbin malaman da aka dauka aikin koyarwa da su zage damtse wajen kawo sauyi mai ma’ana a fannin ilimi domin tabbatar da cigaban yaran yankin.

Ya bayyana hakan ne a wajen bikin mika takardun daukar aiki ga sababbin malaman da aka gudanar a makarantar gwamnati ta ’yan mata (GGASS) Garun Mallam.

A cewarsa, Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya dauki malamai 4,315 domin magance matsalar ƙarancin malamai a jihar tare da inganta harkokin ilimi.

Ya ce, “Ba za mu lamunci sakaci ko wasa da aiki ba. An dauke ku ne saboda an ga jajircewarku da kwazo, shi ya sa gwamna ya amince da daukar ku aikin dundundun a ma’aikatar ilimin bai-daya.”

Tun da farko, sakataren ilimi na karamar hukumar, Alhaji Sabo Muhammad Chiromawa, ya bukaci sababbin malaman da su tabbatar sun kasance malaman zamani masu kawo sauyi a sha’anin koyo da koyarwa domin mayar da karamar hukumar Garun Mallam tamkar yadda aka santa a baya wajen ilimi.

Alfanun Jami’o’in Maryam Abacha ga Al’ummar Nigeria – Daga Shehu Adamu

Ya kuma yi kira gare su da su kasance jakadu na gari ga dalibai da iyaye wajen nuna tarbiyya mai kyau.

A yayin bikin, sababbin malaman sun karrama sakataren ilimi na karamar hukumar da lambar yabo bisa jajircewarsa da sadaukarwa wajen bunkasa ilimi da kuma kyakkyawar mu’amalarsa da ma’aikata.

Bikin mika takardun fara aikin ya samu halartar manyan jami’an ma’aikatar SUBEB na karamar hukumar, iyalai, abokan arziki da kuma jiga-jigan jam’iyyar NNPP na Garun Mallam.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...

Gwamnan Kano ya tura sunayen mutane biyu majalisar dokokin don nada su a mukaman Kwamishinoni

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika...

NLC Reshen Kebbi Ta Soki Cire Naira Miliyan 14 Daga Albashin Malamai

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta...