Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ɗaukar ƙarin malamai na fannin lissafi domin tura su makarantun gwamnati a fadin jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Dakta Ali Makoda, ne ya bayyana hakan yayin bikin raba takardun shaidar karɓar ɗalibai na SS1 a makarantar Sakandare ta Maryam Aloma da ke Kano a yau Laraba.
A cewar sa, wannan mataki ya zama dole ne domin magance ƙarancin malamai da suka cancanta a fannin lissafi a makarantun sakandare.
Makoda ya ce wannan shiri na cikin jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da ingantaccen ilimi kyauta tare da karfafa goyon bayan al’umma ga harkar ilimi.
Ya bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta aiwatar da sauye-sauye da dama, ciki har da ɗaukar malamai, gyaran makarantu, da samar da kayan koyo, domin farfaɗo da tsarin ilimi a jihar.
Kwamishinan ya kuma nuna cewa nasarar Kano na zama jihar da ta fi Kowacce nasara a jarrabawar NECO ta shekarar 2025 ya samo asali ne daga fifikon da gwamna ya baiwa bangaren ilimi.