Gwamna Abba ya amince da a sake ɗaukar malaman lissafi a makaratun Kano

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ɗaukar ƙarin malamai na fannin lissafi domin tura su makarantun gwamnati a fadin jihar.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Dakta Ali Makoda, ne ya bayyana hakan yayin bikin raba takardun shaidar karɓar ɗalibai na SS1 a makarantar Sakandare ta Maryam Aloma da ke Kano a yau Laraba.

A cewar sa, wannan mataki ya zama dole ne domin magance ƙarancin malamai da suka cancanta a fannin lissafi a makarantun sakandare.

Makoda ya ce wannan shiri na cikin jajircewar gwamnatin jihar wajen tabbatar da ingantaccen ilimi kyauta tare da karfafa goyon bayan al’umma ga harkar ilimi.

Ya bayyana cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta aiwatar da sauye-sauye da dama, ciki har da ɗaukar malamai, gyaran makarantu, da samar da kayan koyo, domin farfaɗo da tsarin ilimi a jihar.

Kwamishinan ya kuma nuna cewa nasarar Kano na zama jihar da ta fi Kowacce nasara a jarrabawar NECO ta shekarar 2025 ya samo asali ne daga fifikon da gwamna ya baiwa bangaren ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...