Rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano ta kama wani mutum mai shekaru 33 da ake zargi da zama ɗan sandan bogi domin yaudarar jama’a da karɓar musu kuɗi.
An gano wanda ake zargin mai suna Nasiru Shitu, mazaunin unguwar Kofar Waika a Kano, inda aka cafke shi a ranar Lahadi, 21 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, cikin wani kayan da ake zargin na ƴansanda ne.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda na jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce an kama Shitu ne a Kofar Dawanau, wani yanki da aka sha samun rahoton damfara daga masu ikirarin cewa ‘yan sanda ne.
“Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ba ɗan sanda ba ne, kuma ba ɗan sa-kai na Constabulary ba ne, sai dai mai kwaikwayo da amfani da sunan ƴan sanda domin karɓar kuɗi daga hannun jama’a,” in ji Kiyawa.
Ban taba Nadamar Aiki da Ganduje ba – Abba Anwar
Ya ƙara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu, yayin da ake ci gaba da gudanar da ƙarin bincike domin gano irin yawan laifuffukan da ya aikata da kuma yiwuwar samun abokan harkallarsa.
Kwamishinan ‘Yansanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga jama’a da ke da bayanai ko ƙorafe-ƙorafe game da wanda ake zargin, ko makamantansa, da su tuntubi rundunar ta lambar gaggawa: 07038188127.
Rundunar ta kuma tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar, tare da jajircewa wajen tabbatar da cewa duk masu aikata laifukan damfara sun fuskanci hukunci.