Gwamna Abba ya zargi Ganduje da wawure kudaden Kano ba tare da tabuka komai ba

Date:

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya caccaki tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda ya zarge shi da wawure dukiyar talakawa ba tare da ya yi wani aikin a zo a gani ba.

Da ya ke jawabi a yayin rabon takardar daukar aiki na dindindin ga malaman BESDA su 4, 315, wanda ya gudana a filin wasa na indo a jihar Kano a yau Alhamis, gwamna Abba ya ƙalubalanci Ganduje da ya nuna aiyuka hudu kacal da ya kammala a shekaru takwas na mulkin sa.

Gwamnan ya kuma zargi Ganduje da zaluntar ma’aikata da yan fensho, inda ya ce “da a lokacin su ne da wannan odar ta aiki sigar muku da ita za su yi.”

“Sun zalunci ma’aikata, sun zalunci malaman makaranta da yan fensho.Gashi nan mun taba ofa kuma ba wanda ya bada ko sisi. Mun duba cancanta ne mu ka ɗauke ki aikin nan,” in ji Gwamnan.

Gwamna Abba Kabir ya sake ɗaukar Malamai sama da 4,000 aiki a Kano

Gwamna Abba ya kuma zargi gwamnatin Ganduje da yiwa lalitar gwamnatin jihar karkaf, inda ya ce a takardun mika mulki, ya ga asusun da wani banki ke bin Kano Naira dubu 9.

Ya kuma ce gwamnatin sa na yin mulki ba tare da cin hanci da rashawa na, inda ya ce dalilin da ya sa ta tara makudan biliyoyin Naira a asusun ta kuma da su ake dimbin aiyuka a jihar.

FB IMG 1753738820016
Talla

Gwamnan ya ce yan APC na sukar gwamnatin sa ne saboda suna buƙulun farin jinin ta sakamakon irin ayyukan da take yi a jihar.

A ƙarshe ya hori ma’aikatan da su yi aiki da gaskiya da rikon amana.

Ya kuma umarci hukumar SUBEB da ta ƙara daukar wani rukunin na malaman makarantun firamare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar ODPMNigeria ta shirya taron tattaunawa da matasa a Bichi

Daga Ahmad Isa Getso   Ƙungiyar Rajin Kawo Sauyi da Cigaba...

Yadda Dansanda ya harbe kansa da bindiga a Kano

Wani jami’in dansanda mai suna Aminu Ibrahim ya rasa...

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...