Yan sanda a Kano sun lashi takobin samar da ingantaccen tsaro a ranar Takutaha

Date:

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya taya al’ummar Kano murnar zagayowar watan Maulidi, musamman wajen shagulgulan bikin Takutaha da za a fara ranar Juma’a, 12 ga Satumba, 2025.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24 , CP Bakori ya tabbatar wa jama’ar Kano cewa rundunar ‘yan sanda ta dauki kwararan matakai domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.

Ya jaddada cewa ba za a lamunci duk wani yunkurin tada hankalin al’umma ba, ciki har da fadace-fadacen daba, fashi da makami, kwacen waya da sauran laifuka. Ya ce duk wanda aka kama da sabawa doka zai fuskanci hukunci a gaban kotu.

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Kwamishinan ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro mai dorewa, wanda ya ce shi ne ginshikin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar jihar da kasa baki daya.

Haka kuma, ya gode wa al’ummar jihar Kano bisa hadin kai da goyon bayan da suke baiwa Rundunar, sannan ya tabbatar da cewa rundunar ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyi al’umma.

FB IMG 1753738820016
Talla

Ya bukaci al’umma da su ci gaba da sanya ido tare da bayar da rahoton duk wani motsi ko abun da ba su yarda da shi ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa kamar haka:

08032419754
08123821575
09029292926
A karshe, rundunar ‘yan sandan jihar ta yi wa jama’a fatan alheri da kuma bikin Takutaha cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga...

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...

Yin rijistar katin Zabe zata taimaki addinin musulunci da musulmai – Mal Usman Mai Dubun Isa

Shahararren mai yabon Manzon Allah (S A W) Malam...

Tinubu y ba da umarnin sake Karya farashin kayan Abinci a Nigeria

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wani...