Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da suka shafi auren jinsi da dangoginsa.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar ranar Laraba.
Cikin ƙunshin ƙudurorin da majalisar zartaswar ta aike wa majalisar dokokin – wanda kwamishinan ƙasa da safiyo, Abduljabbar Mohammed Umar ya sanya wa hannu, ta buƙaci da majalisar ta amince da dokar da za ta haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi a a faɗin jihar.
Gwamnatin Kano Ta Ayyana Ranar Hutun Mauludi
Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke amfani da shari’ar addinin musulunci – wadda a dokokinta suka haramta auren jinsi, tare da tanadar hukunci mai tsanani ga wanda ya aikata.