Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana gobe Juma’a, 12 ga Satumba, 2025, wanda ya yi daidai da 19 ga Rabi’ul Awwal 1447 bayan hijira, a matsayin ranar hutu domin bikin Mauludin haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
A cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, gwamnati ta bukaci ma’aikata, ‘yan kasuwa da kuma al’ummar jihar su gudanar da hutun cikin lumana tare da bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
Sanarwar ta kuma yi kira ga jama’a da su yi amfani da wannan damar wajen tunawa da darussa na haɗin kai, juriya da biyayya da kuma koyi da halayen Annabi Sallallahu alaihi wasallam.
Hasashe 6 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kuma suka tabbata a siyasar Kano
Haka zalika, gwamnatin ta shawarci al’ummar jihar da su yi addu’o’i na musamman domin Allah ya baiwa jihar Kano da Nigeria baki daya zaman lafiya da karuwar tattalin arziki.

Gwamnatin jihar ta kuma taya al’ummar Kano murnar bikin Mauludi tare da fatan za a gudanar da shi cikin kwanciyar hankali da lumana .