Musa Iliyasu Kwankwaso na daga cikin fitattun ’yan siyasar Kano da ke da salo na fadin abubuwa a fili ba tare da jin tsoro ba. Sau da dama ana kallon maganganunsa a matsayin siyasa kawai, amma daga baya abubuwan da ya fada na faruwa kamar yadda ya yi hasashe.
Musa Iliyasu Kwankwaso Wanda yanzu haka shi ne Babban daraktan Kudi da mulki na Hukumar Raya Kogunan Hadeja -Jama’are, ya fadin maganganun da a baya ake muku kallon siyasa, wanda yanzu kuma suka tabbata.
Ga wasu jerin hasashe 7 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi wanda kuma suka tabbata .
1. Gargadi kan Kwankwasiyya
Tun kafin zaben 2023, A watan Fabarairu na 2023, Musa Iliyasu ya gargadi jama’ar Kano da kada su mika amanarsu ga Kwankwasiyya ta hanyar zabarsu, yana mai cewa yin hakan zai durkusar da tattalin arziki da kasuwanci a Kano. A yau, ’yan kasuwa na kuka saboda lalacewar harkokin kasuwancinsu, wand hakan yasa mutane suke tunawa da gargadin na Musa Iliyasu.
2. Batun rashawa a Kano
A ranar 12, maris, 2024, Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatin Ganduje ba yi sata ba, idan akai la’akari da satar da gwamnatin Kwankwasiyya za su yi. A dai jira lokaci”
Bayan wani dan lokaci, aka bankado badakalar kayan tallafi da biliyoyin naira a gwamnatin NNPP, abin da ya sa maganarsa ta zama gaskiya.
3. Rashin Tabbas na Siyasa
A ranar 3 ga watan yuni, 2024, Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce baka da tabbacin da wanda za ka yi Siyasar 2027, saboda wasu za su fita daga APC zuwa NNPP kuma haka wasu za su bar NNPP su koma jam’iyyar APC.
Wannan bayani ko hasashen da Musa Iliyasu ya yi ya tabbata domin kuwa ana ta cigaba da chanza jam’iyyu a Wannan lokacin.
Musa Iliyasu Kwankwaso, Rabi’u Sulaiman Bichi sun kama aikin da Tinubu ya ba su
4. Sauyin Sheka
A ranar 7 ga watan Afrilu, 2024 Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya kuma yi hasashen cewa wasu daga cikin ’yan APC da suka fita suka taimaka wa Kwankwasiyya har suka samu nasara za su dawo jam’iyyarsu. yanzu haka ga shi Baffa Bichi da Kawu Sumaila da Kabiru Rurum da Abdulmumin Kofa na daga cikin wadanda suka koma jam’iyyar APC, abin da ya sake tabbatar da hasashen Musa Iliyasu.
5. Rabuwar Baffa Bichi da Kwankwasiyya
A ranar 16, ga watan mayu, 2024 Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi hasashen cewa Baffa Bichi zai fice daga Kwankwasiyya kuma ga shi ya tabbata, bayan da tsohon sakataren gwamnatin ya fice daga jam’iyyar NNPP ya fara sukar shugabanninta tare da barazanar fallasa abubuwan da ya gani a cikin gwamnatin ta Kwankwasiyya.
6. Matakin da Tinubu zai dauka kan tsadar kayan abinchi.
Lokacin da aka fuskanci tsadar Abinchi a Nigeria, A ranar 22, ga watan Yuli, 2024, Musa Iliyasu ya shawarci jama’a da kada su tara abinci, yana cewa Tinubu zai fito da tallafin da zai karyar da kayan abinchi. Kuma haka Kai yanzu haka kayan abinchi kullum sai kara karyewa suke.

A baya-bayan nan, Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaben 2027 da rinjaye, yana mai cewa jam’iyyun adawa ba su da karfin da zasu hana shi cin zabe. Ya kuma gargadi jam’iyyar APC da ta guji rabuwar kai, yana jan hankalin ta da cewa hadin kai shi ne makamin da zai tabbatar da nasararta.
“Tsintsiya guda daya ba ta shara, amma idan aka daure ta, tana iya shara.”
Nigerian Tracker