Gidan Radio Pyramid zai yi aikin hadin gwiwa da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta jihar Kano

Date:

Hukumar gudanarwar gidan Radio tarayya Pyramid FM ta yi alwashin yin aikin hadin gwaiwa tsakanin gidan Radiyon da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta jihar Kano don cigaban al’ummar jihar .

Shugaban gidan Radio Pyramid Dr. Garba Ubale Danbatta ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya Jagoranci Kula alaka da ya Jagoranci Kai shugaban hukumar Dr. Bashir Abdu Muzakkar.

Ya ce la’akari da yadda Duniya ta cigaba komai ya koma amfani da fasahar sadarwa , akwai bukatar gidan Radio da hukumar su hada hannu wajen wayar da kan al’ummar Kano muhimmancin fasahar sadarwa .

Ya ce Babu shakka gwamnan Kano ya yi hangen nesa wajen Samar da hukumar domin za ta taimaka matuka wajen koyawa Matasa Ilimin fasahar sadarwa ta yadda za su inganta rayuwarsu .

Ya ce gidan Radio tarayya zai baiwa hukumar gudunmawa Sosai wajen wayar da kan al’ummar musamman matasa don su rungumi fasahar zamani don gudun kar a barsu a baya.

” Za mu yi Aiki kafa da kafa da Wannan hukumar domin wayar da kan al’ummar domin mun fahimci har yanzu an barmu a baya wajen amfani da fasahar zamani don saukaka aiyuka da inganta rayuwar mu baki daya”.

Ibtila’in: Tsawa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata wata a Kano

Ya ce ” Ina so Wannan hukumar ta Samar mana da wata Cibiyar da zamu rika koyawa ma’aikatanmu Ilimin fasahar sadarwa domin saukakawa da inganta aiyukansu, domin a Wannan zamani dole ne dan jarida ya rika amfani da fasahar zamani don daukaka aikinsa da inganta shi.

Da yake nasa jawabin Shugaban Hukumar Bunkasa fasahar sadarwa ta jihar Kano Dr. Bashir Abdu Muzakkar ya ba da tabbacin hukumar za ta hada hannu da gidan Rediyon Pyramid don wayar da kan al’umma don su fahimci muhimmancin amfani da fasahar zamani .

” Mun zo wani lokaci da dole sai mutane sun rungumi fasahar zamani don inganta aiyukansu da Samun sauki , ko kuma su bari a bar su a baya, domin cigaba kullum zuwa yake yi ko ka bishi ko kuma a barka a baya”. Inji Dr. Muzakkar

FB IMG 1753738820016
Talla

Ya ce duk da cewa hukumar ta su sabuwa ce Amma suna da Tsare-tsare Masu tarin yawa ta yadda za su rika shiga lungu da sako don koyawa mutanen karkara Ilimin fasahar sadarwa da na’urar mai kwakwalwa da dai sauransu .

Dr. Bashir Muzakkar ya ce suna da wani shiri da za su fito da shi Nan ba da jimawaba don dakile kwace wayoyin hannu ta amfani da fasahar sadarwa a jihar Kano baki daya.

Ya kuma yi alkawarin hada hannu da Pyramid Radio don wayar da kan jama’a da kuma tallata manufofin hukumarsu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...