Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa ( NAHCON) ta sanar da aiwatar da sauye sauyen a cikin tsarin ma’aikatar, bayan kammala zamanta Karo na 14, wanda aka gudanar daga 26 zuwa 27 ga watan Augustan, 2025 .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan sashen hulda da jama’a Fatima Sanda Usara ta fitar ranar juma’a.
A bisa matakin ne Hukumar Gudanarwa ta dauka, bangaren zantarwa na NAHCON ya ba da damar mayar da ma’aikatan da aka aro daga wasu ma’aikatu zuwa inda aka dauko su na asali.
An kuma raba takardun shaidar komawarsu ma’aikatunsu na asali
a ranar Alhamis 4 ga watan Satumba, 2025 wannan matakin na daga cikin kokarin kawar da yawan ma’aikatan da ke gararamba da kuma sake tsarin fasalin aikin domin samun ingantacciyar aiki a aikace, haka zalika, hukumar na fatan hakan zai karfafa gwiwar ma’aikata na aiki da kwazo da kuma jajircewa.
A cigaba da sauye- sauyen hukumar ta amince da karin girma ga wasu ma’aikatan da suka cancanta.

hukumar ta kuma amince da shirye -shiryen horaswa da bunkasa kwarewa ga dukkan ma’aikatan domin samun ingantaccen ilimi da kwarewarsu a wajen aiki tare da cimma burin da aka kafa NAHCON domin su.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman ya tabbatar da cewa hukumar za ta cigaba da jajircewa wajen gina kwararrun ma’aikata masu himma domin tabbatar da cewa NAHCON na cika nauyin da dokar kasa ta dora mata na hidimtawa Alhazan Najeriya, ya kara da cewa hukumar za ta cigaba da kirkiro da wasu sauye- sauyen da za su inganta aiki.