Masu Cewa Kwankwasiyya Ta Yi Min Rana Su Sani Nima Na Yi Mata – Dan Majalisar Kiru da Bebeji

Date:



‎Dan Majalisar Wakilai na mazabar Kiru/Bebeji daga jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce ba zai zama abin mamaki ba idan ya fice daga jam’iyyar.

‎Ya kuma ce da arzikinsa ya shiga tsarin Kwankwasiyya, kuma ya bauta mata da kudinsa kamar yadda ita ma Kwankwasiyyar ta taimake shi.

‎A tattaunawarsa da DCL Hausa ranar Alhamis, dan majalisar ya ce shekarunsa sun kai ya san abin da ya fi dacewa da shi kuma ya yankewa kansa hukunci kan abin da fi dacewa da shi.


‎Kofa ya ce, “Ita kanta jam’iyyar ta NNPP ta ce tana nazarin abin da ya dace da ita, saboda haka ba wai dole ne inda jam’iyyar ta nufa na ce dole ni ma can zan bi ba.

‎“Shekaruna sun kai inda zan iya yanke wa kaina hukunci kan abin da ya fi dacewa da ni,” in ji dan majalisar.
‎Sai dai ya ce Kwankwaso maigidansa ne kuma zai ci gaba da girmama shi ko suna jam’iyya daya ko ba sa tare.


‎“Ko ina tare da Kwankwaso ko ba ma tare, ba za ka taba ji na taba shi ba. Shi kansa Gandujen ban taba zaginsa ba don ma tare.

Kungiyar Masu amfani da Ruwan Hadeje-Jama’are ta Zaɓi Sabon Shugaba

‎“Ban taba zuwa neman a ba ni kwangila ba a gwamnatin Kwankwasiyya duk da cewa da ni aka kafa ta. Kwankwasiyya ta yi min rana, amma ni ma na yi mata,” in ji shi.

‎Ya kuma yi zargin cewa babu wanda ya taimake shi lokacin da yake fama da rigimar dakatar da shi da aka yi lokacin da ya zargi jagorancin Majalisar Wakilai a 2016, kan rikicin zargin cushe a kasafin kudi.

FB IMG 1753738820016
Talla


‎Da aka tambaye shi yaushe zai bar jam’iyyar, sai ya ce, “Komai mai iya yiwuwa ne. zan iya tsayawa a NNPP, zan iya barinta, zan iya komawa APC, idan na gad ama na tafi PDP, ko ADC ko ma PRP. Duk inda nake so idan na ga dama zan tafi. A lokacin da na yanke hukunci kowa zai sani.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...