Da dumi-dumi: NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam’iyyar

Date:

Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano ta kori ɗan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, bisa zargin gudanar da ayyukan cin amanar jam’iyya da kuma kasa cika wajibin kuɗin jam’iyya.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa Jibrin, wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai, yayin wata tattaunawa da gidan jaridar DCL a ranar Juma’a inda ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne idan ya bar NNPP.

Haka kuma, ya bayyana cewa ya taimaki jam’iyyar mai mulki wajen lashe zaɓe a Kano, kamar yadda ya koma majalisar wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar a zaɓen 2023.

Sai dai a taron manema labarai da aka gudanar a Kano ranar Asabar, shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Hashim Dungurawa, ya sanar da korar Jibrin, inda ya ce an yanke wannan hukunci ne sakamakon matsanancin suka da Kofan ke yiwa jam’iyyar a kafafen yaɗa labarai kan shugabancinta.

Dungurawa ya bayyana Jibrin a matsayin “ɗan siyasa mara ƙarfi” wanda nasarar zaɓensa ta samo asali ne daga tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP, ba daga ƙarfin kansa ba.

FB IMG 1753738820016
Talla

Shugaban ya ce an kafa kwamiti na sasanci domin tattaunawa da Jibrin bayan hirarsa da tashar talabijin ta Channels , amma fitowar sa ta gaba a kafafen ya tabbatar da cewa ya tsallake iyaka.

“Maimaikon ya zauna a tattaunawa, sai ya ƙara aikata abin da ya sabawa manufar mu, inda ya fito fili ya nuna biyayya ga wani tsari. Shi ya sa muka kore shi. Ba shi da wata gudunmawar da zai bayar,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...