Inganta muhalli: Gwamnatin Kano ta kama wasu mutane bisa zargin sare wasu bishiyoyi

Date:

 

 

Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi ta jihar Kano ta ce a yau ta kama wasu mutane bisa fara sare wasu bishiyoyi a unguwar Na’ibawa, layin Ɗan Hassan a jihar.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce bishiyoyin sun kwashe gwamman shekaru su na bada kariya Da inganta muhalli ga al’ummar yankin.

FB IMG 1753738820016
Talla

Ya ce nan take, aka dakatar da saran bishiyun tare da kama dukkan masu laifin, da kuma kwace kayan aikin hannunsu, ciki har da inji na sare bishiya (chainsaw).

Gwamnatin Kano na neman Karin runfunan zabe a jihar

A cewar Kwamishinan, an mika waɗanda aka kama din ga jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace bisa doka.

Kwamishinan ya kara jaddada cewa sare bishiya ba tare da izinin gwamnati ba babban laifi ne, wanda ka iya jefa mutum cikin gidan yari – ko da bishiyar a cikin gidansa take.

Ya kuma yi gargadi ga duk masu amfani da inji na sare bishiya (chainsaw) ko sauran kayan yankan bishiya ba bisa ka’ida ba, da su sani cewa gwamnati ta haramta hakan, kuma ba za a lamunta da shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...