Shugaban hukumar Kula da aikin hajji ta Nigeria Farfesa Abdullah Sale Usman ya yabawa shugaban Kasa Bola Tinubu bisa yadda ya taimakawa har aka samun nasarori a aikin Hajjin shekara ta 2025.
Farfesa Abdullah Sale ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya jagoranta tare da shugabannin hukumomin Jin dadin Alhazai na Jihohi, domin yin bitar yadda aka gudanar da aikin Hajjin bana da kuma shirin yadda za a gudanar da aikin hajji mai zuwa .

A jawabinsa na bude taron, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewar da yake baiwa alhazan Najeriya da hukumar. Ya yi nuni da yadda Gwamnatin Tarayya ta shiga tsakani wanda ya baiwa masu jigilar Alhazai damar karbar kudade a Naira, tare da kare alhazai daga tashin hankalin kasashen waje.
Gwamnan Kano ya baiwa jami’an tsaro umarnin Kamo yan daban da suka yi sanadiyyar rasuwar hadiminsa
Farfesa Usman ya kuma yabawa Gwamnatin Tarayya bisa umartar Babban Bankin Najeriya (CBN) na baiwa Alhazai kudin guzurinsu a hannu maimakon ta banki.
Shugaban NAHCON ya sanar da cewa duk mai son zuwa aikin hajjin badi zai ajiye kudi har Naira miliyan 8.5 Kafin a kammala tattaunawa da wadanda za su yiwa Alhazan hidima.

Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa a bana ma kasar Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeru Dubu 95,000, kuma za a barwa Kowacce jihar adadin kujerun da aka ba ta a shekarar da ta gabata.
A nasa jawabin, Shugaban kungiyar Sakatarorin Zartarwa na Jihohi, Alhaji Idris Almakura Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Nasarawa (ES) ya gode wa Hukumar NAHCON da ta shirya taron. Ya bukaci hukumar da ta karfafa hadin gwiwa da shuwagabannin jihohi ta hanyar ingantacciyar hanyar sadarwa da kuma yin karin haske kan lokaci.