Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya baiwa jami’an tsaro umarnin Kamo duk wanda yake da hannu a sanadiyyar mutuwar hadiminsa Sadiq Gentle.
“Ina matukar alhinin game da rasuwar Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman a ma’aikatar tarihi da al’adu ta jihar Kano, wanda ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a wani mummunan harin da wasu da ake kyautata zaton ‘yan daba ne suka kai a baya-bayan nan”.

A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Gentle a matsayin “kwararre mai kishin al’umma a kafafen sada zumunta” wanda mutuwarsa ta tashin hankalin gwamnatin jihar da kuma kafafen sada zumunta.
2027: Jonathan zai tsaya takarar shugaban ƙasa don karawa da Tinubu
.
“Na yi matukar bakin ciki lokacin da na Sami labarin rasuwar Malam Sadiq Gentle,” in ji Gwamnan.
Gwamna Yusuf ya yi Allah-wadai da kisan da kakkausar murya, yana mai bayyana shi a matsayin “mummunan abun da ba za a amince da shi ba.”

.
Gwamnan ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan Gentle da abokan arziki da kuma abokan aikinsu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar Kano za ta kasance da su a wannan mawuyacin yanayi.
.