Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya amince da tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2027, in ji wani amintaccen na jikinsa da ke cikin jam’iyyar PDP.
Vanguard ta rawaito cewa na jikin ma Jonathan ya ce, an kai matakin karshe wajen shawo kan Jonathan da ya tsaya takara domin farfaɗo da tattalin arziki da rage wahalhalun jama’a.

Majiyar ta bayyana cewa shirin dawowar Jonathan yana samun goyon bayan manyan shugabanni da dattawan ƙasa waɗanda suka yarda cewa mulkinsa na baya ya kwantar da tarzoma kuma ya daidaita tattalin arziki.
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dasa bishiyu miliyan 5 a jihar
An bayyana cewa Jonathan ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya), da kuma wasu manyan ‘yan siyasa na Arewa da Kudancin ƙasar don neman goyon baya.
Jam’iyyar PDP dai na ƙoƙarin ba Jonathan tikitin takara kai tsaye, tare da wasu jiga-jiganta da suka je Gambia domin shawo kansa.
Jonathan, a halin yanzu, yana ganawa da masu ruwa da tsaki daga yankin Kudu maso Kudu.
Sai dai akwai ce-ce-ku-ce kan ko doka za ta bari Jonathan ya sake takara, kasancewar an rantsar da shi sau biyu.

Amma wasu lauyoyi da wana hukuncin kotu a 2022 sun bayyana cewa gyaran dokar kundin tsarin mulki da aka yi a 2018 ba zai shafi Jonathan ba tunda ya yi mulki kafin gyaran ya fara aiki.
Jam’iyyar PDP na ganin Jonathan zai iya ceto Najeriya daga halin da take ciki, tare da sauya tsarin siyasar ƙasar idan ya amince da takarar.