Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya zargi ‘yansiyasar Najeriya da aikata cin hanci da rashawa saboda “rashin tarbiyya tun daga tasowarsu”.
Da aka tambayi sarkin ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yammacin yau dangane da cin hanci da rashawa, Sanusi ya ce da yawa ba a koya musu yin gaskiya da riƙon amana ba.

“Akasarin mutanen da ke riƙe da ofisoshin gwamnati ba su da wannan tarbiyyar, mafi yawa na shiga gwamnati ne bisa dalilai marasa kyau,” in ji shi.
“Ina ganin an rusa kusan baki ɗayan ɗabi’un kirki na ƙasar nan. Marasa tarbiyya ne suke mulkar mu, waɗanda ba su da wani abin alfahari kuma ba su da niyyar barin wani abin alfahari a bayansu.
“Mutane ne da ke alfahari kawai da yawan dukiyarsu, da yawan gidaje, da yawan jiragen da suka mallaka. Ba su taɓa tunanin cewa mutane na yi musu kallon ɓarayi ne.

“Ba matsalar mutum ɗaya ba ce, shugaban ƙasa ko gwamna. Ku duba yadda shugabannin addininmu suka zama ‘yan bambaɗanci, su ma sarakuna suka kiɗime. Kusan kowa ya auka cikin wannan ruɗanin.”