Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa
Bayan dawowarsa daga garin Madina dake Kasar Saudia Arabia domin jagorantar jana’izar Marigayi Alhaji Aminu Dantata Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya ziyarci iyalan Marigayi Alhaji Aminu Dantata domin yi musu Ta’aziyyar rasuwarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce duniya baki daya ba zata manta da irin gudunmawar da Alhaji Aminu Alhasan Dantata ya bayar ba wajen cigaba a fannoni daban daban.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban sakataren Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikowa Kadaura24.
Mai Martaba Sarkin ya jagoranci gabatar da addu’o’i na musamman ga marigayin inda yayi addu’ar Allah ya jaddada rahama ga Marigayin ya Kuma bawa iyalansa da al’umar jihar Kano da Kasa da duniya baki daya hakurin jure rashinsa.
Da dumi-dumi: Sanarwa ta Musamman daga Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai SKY
Kazalika Mai Martaba Sarkin yakan makamanciyar irin wannan ziyarar Ta’aziyyar ga Hajiya Mariya Dantata inda yayi addu’ar Allah ya gafarta masa ba bashi aljanna madaukakiya.
Kamar kowanne lokaci dai Mai Martaba Sarkin ya samu rakiyar Hakimai da sauran al’umma masoya Sarki tun daga fitowarsa zuwa komawa fadarsa dake gidan Nassarawa a birnin Kano.