Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ba ga Nigeria kadai ba – Mustapha Bakwana

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

Tsohon Mai baiwa gwamnan Kano shawarawa kan harkokin siyasa Hon. Mustapha Hamza Buhari Bakwana ya bi sahun sauran ‘yan Najeriya da na sauran kasashen duniya wajen mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Aminu Alhassan Dantata, hamshakin attajirin kano wanda ya shahara a duniya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hon. Mustapha Hamza Bakwana ya sanyawa hannu da kansa kuma ya aikowa Kadaura24 .

InShot 20250309 102512486
Talla

Sanarwar ta ce ya na mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II da ‘yan kasuwa da kuma iyalan marigayin.

IMG 20250703 WA0023
Mustapha Hamza Buhari Bakwana tare da Alh. Aliko Dangote

Bakwana ya bayyana rasuwar Alhaji Dantata a matsayin babban rashi ga ‘yan kasuwar duniya, musamman na yankin Sahara.

Ya kara da cewa al’umma da dama sun amfana da arzikinsa ta hanyar ba su aiyukan yi a kamfanoninsa da kuma aiyukan jin Kai da ya rika gabatarwa a cikin al’umma.

An yi gangamin yaki da fadan daba, kwacen waya da shaye-shaye Unguwar Tudun wada

Bakwana ya ce “ba shakka za a rika tunawa da marigayi Dantata a matsayin daya daga cikin wadanda suka ba da gudunmawa sosai wajen ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, musamman Kano, cibiyar harkokin Kasuwanci Arewacin Nijeriya.

Ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya saka masa da kyawawan ayyukansa da aljannah firdausi sannan ya bukaci ‘yan uwa da abokan arzikinsa da su yi hakuri da Wannan Babban rashin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Janar Manaja na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...