Daga
Tsohon Ministan shari’a na Nigeria zamanin mulkin Buhari Abubakar Malamin ya fice daga jam’iyyar APC inda ya koma jam’iyyar ADC ta masu kokarin kawar da Tinubu daga shugabancin Kasa .
Abubakar Malami ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook.
Ga rubutunsa :

Assalamualaikum wa rahamatullahi ta,ala wa barakatuhu, ’Yan uwa da abokan arziki na Jihar Kebbi da Najeriya gaba ɗaya,
Bayan dogon tunani da shawarwari da dama da muka dauki lokaci munayi, na yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma na karɓi sabuwar tafiya a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), jam’iyyar da hadakar sabbin jagorori da masu kishin Najeriya suka amince da ita a matsayin mafita ga halin da ƙasar mu ke ciki.
Na ɗauki wannan mataki ne saboda halin da ƙasarmu ta tsinci kanta a ciki. A halin yanzu, Najeriya na fama da matsaloli da dama da suka shafi tsaro, tattalin arziki da kuma gazawar gwamnati wajen gudanar da shugabanci mai ma’ana.
A Arewa, mun wayi gari da tsoron fita kasuwa ko gona saboda harin ‘yan bindiga da satar mutane. Rayukan jama’a na salwanta, amma gwamnati ta zabi yin shiru ko kuma ta maida hankali kan rikicin cikin gida da siyasar son zuciya.
Tattalin arzikin ƙasa kuma ya shiga wani mawuyacin hali. Farashin kayan masarufi ya tashi fiye da kima. Talaka ba ya iya cin abinci sau ɗaya a rana. Matasa sun rasa aiki, al,amurra . Cire tallafin mai ba tare da tanadin saukaka wa al’umma ba ya kara jefa mutane cikin tsananin ƙunci.
Magance sheye-shaye ne kadai zai kawo karshen matsalar tsaro da talauci a Nugeria – Shugabar LESPADA
Gaskiya ita ce, an ajiye shugabanci a gefe, an rungumi siyasa. An bar muradin talaka, an rungumi faɗa da juna da son rai. Wannan ba shi ne burin da muka fara tafiya da shi a APC ba, kuma ba zan iya ci gaba da zama cikin irin wannan tsarin da ke jefa rayuwar al’umma cikin hatsari ba.
Shigata ADC ba gudu ba ne, ba fushi ba ne. Wannan mataki ne na kishin ƙasa da yunkurin dawo da martabar shugabanci a Najeriya. Jam’iyyar ADC na da tsari da hangen nesa da ya dace da muradinmu na gaskiya, adalci, da ceto ƙasa.
Ga jama’ar Jihar Kebbi, ku sani cewa ban bar ku ba. Har yanzu ni ɗanku ne, kuma zan ci gaba da zama tare da ku, ina wakiltar muradunku da kare hakkinku kamar yadda kuka sani ni.
Ga ’yan Najeriya gaba ɗaya, lokaci ya yi da za mu tsaya mu ce “ya isa!” Mu nemi canji na gaskiya, ba canjin suna kawai ba. Mu tashi tsaye mu kwato ƙasarmu.
Allah ya albarkaci Jihar Kebbi. Allah ya albarkaci Najeriya.
Na gode.
Abubakar Malami, SAN
2 Ga Yuli, 2025