Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar sun mayar da jana’izar Alhaji Aminu Dantata zuwa bayan Sallar Maghariba .
Ministan yada labaran Nigeria Muhammad Idris ne ya bayyana hakan ga gidan Radio BBC .

Ya ce tun da sanyin safiyar Wannan Rana ta talata ne aka Kai gawar Marigayin bayan da Kasar ta Saudiyya ta Amince da Binne Marigayin .
Idan za a iya tunawa da sanyi safiyar Wannan Rana ta talata aka ce za a yi jana’izar da la’asar , Amma aka sauya lokacin zuwa Magaribar Wannan Rana