Hukumar kula da almajirai ta Kasa ta kaddamar da yiwa almajirai Rijista a Kano

Date:

Daga Saminu Ibrahim Magashi

 

Hukumar kula da almajirai da yaran da ba sa zuwa Makarantar ta gwamnatin tarayya ta yi gangamin kaddamar da yi wa almajirai kimanin su 200 rijista a kano.

Da yake jawabi a yayin taron shugaban hukumar na kasa Dr. Muhammad Idris ya bayyana cewa sun ɗauki matakin yiwa almajirai rijista ne domin Sanin hakikanin tawansu don tallafawa rayuwarsu da ingantata.

InShot 20250309 102512486
Talla

“Wannnan ya na daga kudirin gwamnatin tarayya mai ci na tabbatar da cewa kowanne yaro da ya kamata ya Sami ulimin da ya dace , don haka ta lashi takobin mayar da yaran da ba sa zuwa Makaranta zuwa Makarantar”. Inji Dr Muhammad Idris

Ya ce wannan ne karon farko da aka kaddamar da fara yi wa almajiran rijista, kuma ya ce za su tabbatar da cewa sun cikawa shugaban kasa muradinsa na koyar da ya’yan al’umma kyauta tare da daukar nauyin malaman da za su rinka koyar da su.

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

“Za mu koyawa yaran harsunan larabci da turanci domin tabbar da cewa su ma sun sami gogayya tsakaninsu da sauran ya’yan al’umma”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

A jawabinsa wakilin Yamma malam Aminu Tijjani Sunusi ya bayyana matukar farin cikinsa tare da rokon wannan hukuma da ta rubanya wannna kokarin na ta acikin qaramar hukumar gwale tayanda kowacce mazaba zata rabauta da wannna tsari.

Gangamin yin rigistar ya gudana ne a filin unguwar galadanci dake karamar hukumar Gwale ya kuma samu halartar muhimman mutane ciki har da masu unguwannin yanki, iyayen Yara da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da gudu zan karɓi tayin kujerar mataimakin shugaban ƙasa – Barau Jibrin

Daga Isa Ahmad Getso Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata...

Inganta tsaro: Shugaban K/H Tarauni ya ba da fili domin gina ofishin Civil Defence a karkasara

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed...

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam...

Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga...