Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Malam Adamu Yusuf Tofa a matsayin Babban Mai taimaka masa na musamman kan Ilimin Tsangaya, da kuma Hon.Surajo Ahmad Chedi a matsayin mai bashi shawara kan ci gaban harkokin alʼummar karkara.
Wannan na cikin wata sanarwa da Babban Darkatn Yaɗa Labaran Gwamnam Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Sanarwar ta ce Malam Tofa tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Tofa ne, Kuma kwararre a ilimin addinin Musulunci da tsarin Tsangaya.
Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci
Haka kuma Hon.Chedi tsohon kansila ne mai gogewa a harkokin al’umma.
Sanarwar ta Kara dacewa Gwamnan na ganin waɗannan nade-naden na daga cikin matakan kara shigar da kowa a tafiyar gwamnati, musamman jama’ar karkara da masu bukata ta musamman.