Daga Isa Ahmad Getso
Mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya ce da zaran shugaban ƙasa Bola Tinubu ya mika masa gayyatar zama mataimakinsa a zaben shekarar 2027 da gudu zai karɓa
Barau wanda ke ganawa da manema labarai a Abuja, ya ce a shirye yake ya sadaukar da kansa domin gudanar da duk wani aikin da shugaban ƙasar ya ba shi.

Sanatan wanda ya bayyana cewar ba ya buƙatar yin dogon jawabi dangane da lamarin a halin yanzu, ya ce lokaci bai yi ba da jama’a za su dinga tallata shi domin zama mataimakin shugaban ƙasa a zabe mai zuwa.
Barau ya ce bai ma san waɗannan ƙungiyoyin dake tallata shi ba, amma kuma ya buƙace su da su mayar da hankali wajen tallata ayyukan da shugaban ƙasa Tinubu ke yi da kuma goya masa baya.
Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-nade
Sanatan ya ce da zaran lokacin siyasa ya yi, za su sadaukar da lokutan su domin tinkarar duk wani kalubale, yayin da ya ƙara da cewar yanzu lokaci ne na mulki amma ba na siyasa ba.
Jaridar Vanguard ta ce Barau ya bayyana Tinubu a matsayin shugaban da ya samar da ci gaba da dama a bangaren siyasa, ciki harda taimaka masa wajen komawa Majalisa da kuma zama mataimakin shugaban majalisar.
Saboda haka, Sanatan ya ce da zaran Tinubu ya ce masa ga aikin da yake so ya yi, a guje zai karɓa, kuma yana tabbatar da goyan bayan sa ɗari bisa ɗari ga shugaban.
A makwannin da suka gabata ne, baraka ta fito fili tsakanin ƴayan jam’iyyar APC mai mulki dangane da kujerar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a zabe mai zuwa.
Gwamnatin Kano ta bada hutun sabuwar shekarar Musulunci
Wannan ya haifar da ruɗani a taron da jiga jigan jam’iyyar suka gudanar a shiyar arewa maso gabas, wadda ta kai ga bai wa hammata iska.

Tun bayan lokacin ake rade radin cewar Tinubu zai sauya mataimakinsa Shettima a zabe mai zuwa, yayin da aka fara bayyana sunayen wasu fitattun ƴan siyasa daga ƴankin arewa maso yamma a matsayin waɗanda ake hasashen na iya samun kujerar.
Wata majiya kuma ta ce daga cikin masu neman kujerar a ƙarƙashin ƙasa har da wasu gwamnonin arewa maso gabas dake kammala wa’adin mulkin su a shekarar 2027.
Wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC sun ce shugaba Tinubu ne kawai ke da hurumin zaben wanda zai mara masa baya, kuma hakan zai faru ne da zaran jam’iyyar ta tabbatar masa da kujerar takarar a taron zaben fidda gwanin da za’ayi.
Ya zuwa yanzu dai, ƴan siyasa da wasu jama’ar Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da wannan dambarwar wadda ake ganin ka iya raba kan jam’iyyar.