Iftila’i: Bam ya fashe a Kano ya hallaka wasu ya kuma jikkata wasu

Date:

Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Jihar Kano.

Daily trust ta gano yadda fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki.

InShot 20250309 102512486
Talla

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke yin jigilar ne wanda aka yi sakaci ya fashe.

Lamarin dai ya faru ne a bypass dake jihar Kano.

“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin kamar bama-baman sojoji ne suka fashe.

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

“Mutane 15 sun jikkata, kuma abin takaici, guda biyar sun rasu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa yankin domin samun kulawa ta gaggawa.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da kayan fashewar, wadda ta ke kan hanyar zuwa Jihar Yobe.

Har yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da ko motar sojoji ce ke ɗauke da kayan fashewar ba.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Rundunar na ci gaba da da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma abin da ya haddasa fashewar abun.

“Za mu samu cikakken bayani bayan kammala bincike,” in ji Kwamishinan.

Ya kuma roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta sami wani Tela da laifin takurawa makwabtansa da karar keken dinki

Wata kotu a Kano ta samu wani tela da...

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...