Shugaban K/H Wudil ya taya Kungiyar Kwallon Kafa ta Kwankwasiyya Academy murnar Nasara da ta samu

Date:

Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba Muhammad Tukur, ya taya kungiyar kwallon kafa ta Kwankwasiyya Academy ta Wudil murnar nasarar da suka samu akan Karaye Academy a wani wasa da suka gudanar a safiyar jiya alhamis a Kaduna. Ya yabawa ’yan wasan da jami’ai bisa ga bajintar da suka yi, da da’a, da kwazo.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban sakataren yada labaran shugaban karamar hukumar Nura Mu’azu Wudil ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hon.Abba Tukur ya bayyana nasarar a matsayin abin alfahari ga daukacin al’ummar karamar hukumar Wudil musamman saboda yadda matasan Wudil suke nuna hazaka, da kwazo akan abubuwan cigaba .

Ya kuma godewa dukkanin yan tawagarsa ciki har da ‘yan majalisar karamar hukumar, da daraktan kula da ma’aikata, da sauran ma’aikata bisa goyon bayan da suka bayar a lokacin gasar.

Zargin cin Bashi: Gwamna Abba bai taba ciyo bashi ba – Gwamnatin Kano

Shugaban ya kuma mika sakon taya murna ta musamman ga Abba Sale da Dan Isi, fitattun ‘yan wasan kungiyar wadanda aka zaba domin shiga kungiyar kwallon kafa ta jiha da Kasa .

Hon. Abba Muhammad Tukur ya kuma ba da kyauta Kudi har Naira dubu 100 ga golan kungiyar Khaleefa Keshon saboda bajintar da yayi na hana kwallo ta shiga ragarsu.

Hon. Tukur ya kara jaddada kudirin gwamnatin sa na ci gaba da tallafawa matasa da wasanni, inda ya yi alkawarin kara saka hannun jari a harkokin Matasa domin bunkasa hazakarsu.

InShot 20250309 102403344

A karshen taron, shugabannin kananan hukumomin Fagge, Rano, Tsanyawa, da Karaye sun yaba da jajircewar da Abba muhammad Tukur ya yi wajen bunkasa harkokin wasanni a Wudil

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...