Daga Nazifi Bala Dukawa
Kungiyar cigaban garin Rimin Zakara ta musanta zargin da Sakataren kungiyar Mustapha Aliyu ya yi na cewa gwamnatin Kano na kokarin sake yin rusau a garin.
Babban limamin garin malam Rabi’u Zakariyya ya ce Babu kamshin gaskiya a labarin da tsohon skataren Kungiyar ya sanar na yin rusau a garin, inda su ka ce ya yi ne a kamshin kansa kuma babu wani labarin russau da suka samu .

Haka zalika limamani garin ya ce tuni suka sauke shi daga mukamin sakataren kungiyar cigaban garin na Rimin Zakaria.
Shi ma shugaban matasan garin magaji idiris ya ce waccen magana babu ita su a saninsu garin ya zauna lafiya zuwa yanzu Kuma basa tare da waccen magana.
Malam shua’aibu mahammmad guda ne cikin shugabanin garin ya ce waccen magana Babu ita Kuma masu fadin hakan ba sa kishin garin don haka basa goyon bayan wacce kalamai kuma Babu saninsu ya gabatar da waccen magana Kuma suna tare da duk abinda gwamnnatin jihar kano yazo dashi
Alh baba habu mika’ilu rimin zakara shugaban Kungiyar cigaban garin rimin zakara yace wanna Jan fenti da aka gani a jikin gidaje anyi ne don kidaya gidajen yankin don Samar da cigaban garin kamar yadda a baya gwamnan kano ya samar da wutar lantarki a garin Kuma basa goyon bayan faruwar Wani Abu mara dadi daya faru a Nan gaba Kuma hankalin kowa ya kwanta don sun San cewa gwamnnatin tana da burin taimakawa garin.
Karshen Baba habu ya yabawa gwamnan kano kan yadda ya Samar da wutar lantarki da asibiti akan kudin miliyan sama da dari biyu 200 da makaranta da sama da miliyan dari 300 don Samar da massalacin a gari da ware sama da biliyan daya don cigaban garin.