Zargin cin Bashi: Gwamna Abba bai taba ciyo bashi ba – Gwamnatin Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin jihar Kano ta musanta zargin da wata kungiyar jam’iyyar APC mai suna APC Patriotic Volunteers Group ta yi na cewa Gwamnatin ta bashi Kasashen waje da ya Kai Dala Miliyan 6 da digo 6 ($6.6m) a cikin shekaru 2 .

“Abun mamakin shugaban Wannan kungiya da ta yi wancan zargi a lokacin da aka yi dokar Wannan hukumar shi ne Sakataren gwamnatin jihar Kano kuma mai gidansa Gwamna Kano a wancan lokacin Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya sanyawa dokar hannu a shekarar 2021”.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban hukumar Kula da basussuka ta jihar Kano Hamisu Sadi Ali ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

” Akwai Mamaki ace Usman Alhaji wanda ya yi sakataren gwamnatin Kano ya ce bai san dokokin hukumar Kula da basussuka ta jihar Kano ba, to idan Bai Sani ba ko kuma ya manta to bari mu tuna masa sashi na 4(b) na dokokin hukumarmu da ya yi bayani karara cewa hukumar tana da hurumin ciyo ba shi a madadin gwamnatin jiha daga wuri Cibiyoyi, hukumomin ko kuma daidaikun jama’a”.

Gwamna Abba ya jinjinawa hukumomin ba da agajin gaggauwa, bisa dakile iftila’i tankar Mai a Kano

Ya ce kuma doka ta yi bayani karara cewa gwamnatin ba ta da hurumin ciyo bashi ko da na sisin kobo ba tare da Sanin hukumar Kula da basussuka ta jihar Kano ba.

Sanarwar ta kara da cewa ” bari na yi bayani karara kowa ya ji, tunda gwamnatin jam’iyyar NNPP ta hau mulkin Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf ko sau daya ba a tuntubi wanna hukumar da niyar za ta ciwo bashin cikin gida ko na Kasashen waje ba, Hasali ma kokari muke mu biya basussukan da gwamnatin Ganduje ta ciyo a kasashe.

InShot 20250309 102403344

Ya kara da cewa ya kamata Usman Alhaji ya Sani mutanen Wannan lokaci mutane ne masu Ilimi da wayo , ba yarda za ka yi kazo da wani zargi akan wani ba tare da ka zo da hujja ba kuma mutane su yarda.

Ya ce wannan zargin na ku ba zai tsayar da Gwamna daga aiyukan da ya yake yiwa al’ummar jihar Kano, kuma Muna kira ga al’ummar jihar Kano da na kasa baki daya da su yi watsi da zargin Usman Alhaji da yan baran dansa, domin zargi ne mara tushe ballantana makama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...