Daga Rayyan Hassan
Al’ummar garin Rimin Zakara dake karamar hukumar Ungoggo a jihar Kano sun koka da cewa wasu mutane sun sake zuwa garin suna sanya musu Jan fenti a wasu daga cikin gidajensu wanda hakan ya jefa su cikin hadin dar-dar.
” A baya an yi mana makamancin irin wannan kuma gwamnan Kano da Sarkin Kano sun zo sun yi mana abubuwan da suka gabata , Amma kuma yanzu ga shi an sake dawowa, Amma dai har yanzu ba mu ma tabbatar da su waye ba”.

Mustapha Aliyu Alhasan Rimin Zakara ne ya bayyana hakan a wata ganawa da yayi da wakilin Jaridar Kadaura24 yau Alhamis a Kano .
Ya ce sun damu matuka da yadda suka ga wasu mutane da suka ce daga ma’aikatar Kasa da tsare-tsare su ke suka zo suna sanya musu Jan fenti a jikin gidajensu.
Zargin cin Bashi: Gwamna Abba bai taba ciyo bashi ba – Gwamnatin Kano
“Muna kira ga gwamnan Kano da ya sanya baki saboda wannan abun da aka zo ana yi ya daga hankalin mutanen Rimin Zakara kwarai da gaske, abun da muke gudu shi ne kada wani abu irin wannan ya faru a baya ya sake faruwa ko ma fiye da haka saboda yanzu kowa zuciyarsa a kusa ta ke”. A cewarsa
Mustapha Rimin Zakara ya ce su kuma rokon mai girma gwamnan Kano da ya dubu kokensu ya sa ayi bincike Kan wannan lamarin don tabbatar da zaman lafiya.
Ya ce amadadi al’ummar garin Rimin Zakara suna yabawa gwamnan Kano kan Matakai da aiyukan da ya Fara yi musu a baya, inda suka ce sun tabbatar da cewa gwamnan mai fada da cikawa ne.
Kadaura24 ta tuntubi Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar da Kasa da tsare-tsare ta jihar Kano Umar Abdu Kurmawa don jin ta bakinsu kan wannan batu, sai dai ya ce ba shi da masaniya kan batun Amma mu ba shi lokaci zai bincika.