Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba kabair Yusuf ya yabawa hukumomin ba da agajin gaggawa na jihar Kano bisa yadda suka yi nasarar dakile yiwuwar fashewar wata tankar man fetur a hanyar BUK zuwa Gwarzo ranar Laraba.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Lamarin ya faru ne a kusa da mahadar sakatariyar hukumar NYSC, inda wata tankar dakon man fetur ta burma rami lokacin da take kokarin shiga gidan mai, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar gobara a yankin.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Yusuf ya bayyana matukar godiya ga hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) RS1.2 Kano, hukumar kashe gobara ta tarayya, kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano (KAROTA) bisa gaggarumar rawar da suka taka.
Rikici: Dan Majalisar NNPP ya zargi Sanusi Bature da yi wa Gwamnan Kano zagon kasa
Gwamna Yusuf ya yaba da hadin gwiwa a tsakanin hukumomin wajen dakile faruwar hatsari ko Wani iftila’i.
Ya kuma yi kira ga direbobin tankar mai da masu aikin mai da su kiyaye ka’idojin kariya a lokacin da ake yin lodi da sauke kaya domin kaucewa hadurra a nan gaba.
Da yake nanata kudurin gwamnatinsa na tabbatar da tsaron jama’a, Gwamna Yusuf ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da karfafa hanyoyin bayar da agajin gaggawa da inganta hadin gwiwar hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin daukacin mazauna Jihar.