Daga Abba Idris
An samu tsaiko wajen gudanar da harkokin sufuri akan titin Gwarzo.
Hakan ya biyo bayan burmawar wata tanka Dakon mai dake kokarin sauke Mai a wani gidan mai dake daura da Headquartar Matasa masu Hidimar Kasa dake Rijiyar Zaki.

Wakilin mu Abba Salisu Idris Daya ratso ta wajen ya ruwaito cewa an datse hannu Daya na Babban titin tun Daga janbulo zuwa Rijiyar Zaki inda masu ababen Hawa dake zirga zirga da matafiya ke aron hannu Suna bin hannu Daya na titin.
Da dumi-dumi: Tinubu zai yi wa yan Nigeria jawabi
Da wakilin namu Abba Idris ya tattauna da wasu matafiya sun baiyyana cewa sun shafe Fiye da mintuna ashirin Daga tsohuwar jami’ar Bayero zuwa kabuga sakamon cunkosan ababen Hawa, yayinda wasu Kuma masu ababen Hawan ke bin ratse domin kaucewa cunkosan ababen Hawa.
Tini dai aka jigbge jami’an tsaro domin kare Juma’a dake hankoran zuwa wurin motar tankar.
Haka zalika Tini motocin bada agaji na kashe gobara Dana Asibiti Dana bada agajin gaggawa suka Isa wurin domin jiran Kota kwana kawo lokacin da muke hada muku wannan rahotan ana can ana kokarin Mai da man zuwa wata Tankar.