Kungiyar Shekarau ta gindaya Sharadi Kafin shiga hadakar yan adawa a Nigeria

Date:

Ƙungiyar League of Northern Democrats (LND) ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ta bayyana cewa sai an kafa sabuwar jam’iyyar siyasa ne za ta shiga cikin haɗakar ‘yan adawa da ke shirin korar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu daga mulki a zaɓen 2027.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Shugaban ƙungiyar, Dr. Umar Arɗo, tare da wasu manyan mambobi 12, sun bayyana hakan cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Lahadi, inda suka ce sun duba zaɓi biyu da ake da su — shiga cikin jam’iyyar ADC ko SDP, ko kuma kafa sabuwar jam’iyya daga tushe.

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Sanarwar ta nuna cewa duk da ana raɗe-raɗin cewa haɗakar ‘yan adawa ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar da tsoffin gwamnoni irin su Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi za su yi amfani da wata tsohuwar jam’iyya, amma ƙungiyar LND na ganin hakan zai iya jawo rikice-rikice da rikicin shugabanci.

InShot 20250309 102403344

Arɗo ya bayyana cewa, “Jam’iyyun da ke akwai irin su ADC da SDP suna da tsarin shugabanci da aka kafa bisa doka wanda sau da yawa ba ya karɓar sauyi. Misali, shugaban ADC a Adamawa ya ce wa’adinsa yana nan daram har zuwa Disamba 2026. Wannan yanayi ne da ke akwai a sassa daban-daban na ƙasa.”

A cewarsa, kafa sabuwar jam’iyya zai bayar damar samar da sabon tunani da tsari, da kuma sabunta siyasa wanda zai iya karɓuwa a zuƙatan ‘yan Nijeriya da suka gaji da tsoffin jam’iyyu da alƙawarin da ba a cika ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...