Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kungiyar ma’aikatan Radio da Talabijin ta kasa reshen jihar Kano (RATTAWU) ta ce tana mika sakon ta’aziyya ga iyalai da yan uwan mutane 22 da suka yi hatsarin dake cikin tawagar wakilan jihar Kano a gasar wasanni ta Kasa a ka gudanar a jihar Ogun.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar reshen jihar Kano Comrade Babangida Mamuda Biyamusu ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Sanarwar ta baiyyana matasan a matsayin zakakurai kuma “yan kishin jihar kano wanda tarihin kano ba zai taba mantawa dasu ba.
Comrade Babangida Mamuda Biyamusu ya baiyyana cewa daukacin ‘ya’yan kungiyar ta RATTAWU sun nuna jimamin su da Babban rashin tare da addu’ar Allah ya gafar ta musu yasa aljannatul Firdausi ce makomar su ya kuma baiwa iyalan su hakurin jure Babban rashin ya kuma tashi kafadun wadanda suka jikkata.
Sanarwar ta aike da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan da gwamnan kano da Mai martaba sarkin kano da ma’aikatar matasa da wasanni dama al’umma jihar Kano baki daya.