Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan makarantun Firamare da na Sakandare a fadin jihar da su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025 zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban makarantu kwana, sannan daga ranar Laraba 4 ga Yuni, 2025 zuwa Litinin 16 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban da ke zuwa gida bayan makaranta.

Wani jawabi da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru ya sanya wa hannu ya bayyana cewa iyaye da masu kula da ɗaliban makarantun kwana su je su ɗauki ‘ya’yansu da sassafe a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Sanarwar ta nakalto Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Makoda yana kira ga iyaye da masu kula da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun dawo makaranta a ranar da aka tsara, tare da gode musu bisa goyon baya da hadin kai da suke bai wa ma’aikatar.

InShot 20250309 102403344

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah Za ta Tura Sama da Jami’ai 1,000 Don Samar da Tsaro a Ranar Takutaha a Kano

Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano...

Kotun tafi-da-gidanka ta KAROTA ta ayyana neman wani direba ruwa a jallo

Alkalin Kotun Majistare da ke gudanar da shari’ar masu...

Muna rokon gwamnatin Kano ta haramta daukar fasinjoji a bakin titi – Kungiyar Direbobin Haya

Ƙungiyar Direbobin Motocin Haya ta ƙasa reshen Kano dake...

Rijistar Zabe: Gidan Rediyon Kano Ya Ƙara Zage Dantse Wajen Wayar da Kai Kan Al’umma

Hukumar gudanarwar Gidan Rediyon jihar Kano ta ƙara kaimi...