Daga Halima Umar Dogo
Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba Yawale ya bayyana cewa tsohon Dan takarar Sanatan kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Abdulssalam Abdulkareem wanda aka fi Sani da A A Zaura shi kadai ne mutum daya tilo a jihar Kano da ya ke taimakawa al’umma ba tare da neman wani mukamin gwamnati ba.
“Ya na kokarin baiwa ‘ya’yan talakawa fifiko wajen samar musu da rayuwa mai inganci, musamman wajen dakile fadan Daba da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano”.

Alhaji Baba Yawale ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Ya ce A A Zaura ya sadaukar da rayuwarsa wajen samar wa al’ummar jihar kano musamman matasa rayuwa mai kyau.
Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben kananan hukumomin Kano
“Muna kira ga al’ummar Jihar Kano da su ba shi goyon baya wajen ganin ayyukan da yake yi don ci gaban Jiharmu ta Kano ya Sami nasarar da ake fata.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a Yan kwanakin nan bayan dawowar fadan daba a Kano , AA Zaura ya dage Yana ta tattaunawa da masu ruwa da tsakin domin ganin yadda za a kawo karshen fadan daba a fadin jihar Kano.
Da sauran Shugabannin al’umma a jihar Kano za su hada kai da A A Zaura da an sami nasarar kawo karshen fadan Daba da yaki ci yaki cinyewa a jihar Kano , musamman a kananan hukumomin dake kwaryar birnin jihar.