Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin cikinta da gamsuwarta bisa hukuncin da kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yanke, wanda ya yi watsi da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke a baya na neman dakatar da gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

Kadaura24 ta rawaito a hukuncin da ta yanke, Kotun daukaka kara, karkashin jagorancin Mai shari’a Oyewumi, ta bayyana cewa babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari’ar da ta shafi gudanar da zaben kananan hukumomi.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Tun da farko dai jam’iyyar APC da kuma wani bangare na jam’iyyar NNPP ne suka shigar da karar, inda su ke kalubalantar sahihancin zaben, inda suka zargi shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, Farfesa Sani Lawan Malumfashi da cewa Dan Siyasa ne.

Da take yanke hukunci a kan lamarin, kotun daukaka kara ta amince da karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar tare da soke hukuncin da karamar kotun ta yanke. Wannan hukunci ya tabbatar da cewa zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a jihar na da inganci kuma an yi zaben akan doka.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya aikowa Kadaura24, ya ce gwamnatin Kano ta kalli wannan hukunci a matsayin nasara ga dimokuradiyya, da cewa zai kawo hadin kan al’ummar jihar Kano baki daya.

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben kananan hukumomin Kano

Har ila yau, ya yabawa bangaren shari’a bisa adalcin da suka yi a shari’ar wanda ya ce hakan zai kara tabbatar da cewa mulkin dimokradiyya ya zauna Sosai.

“Hukuncin ya kara tabbatar da kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha, na gudanar da sahihin zabe, wanda ya samar da zababbun shugabannin kananan hukumomi 44 da kuma Unguwani 484 na jihar”. A cewar sanarwar

InShot 20250309 102403344

Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa bangaren shari’a bisa jajircewa da adalcinsu wajen tabbatar da ana bin kundin tsarin mulkin Nigeria. Ya kuma yabawa al’ummar jihar Kano bisa natsuwa da juriya da hakurin da suka nuna a yayin da suke jiran sakamakon shari’a.

Gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta samar da ci gaba tun daga tushe sannan kuma za ta ci gaba da tallafawa kananan hukumomin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya don isar da ribar dimokuradiyya ga al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan zaben kananan hukumomin Kano

Kotun ɗaukaka kara dake Abuja, ta rushe hukuncin babbar...