Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cewa ta kama mutanen da ake zargi da kisan gillar da aka yiwa Babban baturen yan sanda na karamar hukumar Rabo.
Ya bayyana alhini da jimami bisa mummunan kisan gillan da aka yi wa Baturen ‘Yan Sanda na Rano (DPO), CSP Baba Ali, yayin da yake bakin aiki.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar Yansandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai.

Rundunar Yan Sandan ta kalli Wannan kisa na rashin hankali da al’umma suka masa mummunar suka a matsayin mummunan hari ga zaman lafiyar al’umma da kuma cin mutunci ga jajircewar jami’an ‘yan sanda da ke fuskantar haɗari kowace rana don kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Mun Gamsu da Samar da Kungiyar Kwarya ta bi Kwarya -Mai Rago
Sai dai Rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa an gurfanar da duk masu hannu a wannan ta’asa a gaban kotu. Bayan gudanar da bincike, an kama mutane 41, ciki har da wadanda aka same su dumu-dumu da hannu a cikin lamarin.
‘Yan sanda na ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da cewa ba a bar kowa ba cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, sfipma, mnim, mnips, masis, ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar zata cigaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin Jihar bakidaya. Ya sake nanata cewa ba za a bar kowanne mai hannu a wannan ta’asa ba har sai an gurfanar da shi a gaban shari’a.
Rundunar na godiya ga fahimta, ta’aziyya da hadin kai da jama’a ke basu, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da zama cikin natsuwa da bayar da cikakken goyon baya ga ‘Yan Sanda a wannan bincike. Za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen kare al’umma, tare da tabbatar da cewa duk wanda ya nemi dagula zaman lafiya, za a hukunta shi yadda ya kamata.
Hakazalika, rundunar ta karrama marigayi CSP Baba Ali, tare da yabawa jarumta da sadaukarwar jami’anmu da ke ci gaba da fuskantar haɗura don kare jihar mu.