Daga Maryam Muhammad Ibrahim
A wani salo na tabbatar da doka tare da kawo tsafta a bangaren Dab’i, Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh. Abba El-mustapha ta kara yin nasarar ganowa tare da kama wasu na’urori da ake amfani dasu wajan buga hotunan batsa ga masu sana’ar maganin Gargajiya a cikin wasu unguwannin Jahar Kano wanda suka hada da komfuyutoci da Kuma injinan buga hotuna wato (Printers).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikowa Kadaura24.
Da yake holan kayan da Hukumar ta kama Alh. Abubakar Zakari Garun Babba darakan Dab’i na hukumar ya bayyana guraren da aka kama wannan kaya sun hada da wasu unguwani a karamar Hukumar birnin da Kuma wasu kauyuka na karamar Hukumar Wudil.

Garun Babba ya nuna taikacinsa kan yadda wasu ke fakewa da Sana’ar buga takardun watau photocopy inda suke buga hotunan batsa, inda ya kara da cewa ko kusa ko alama Hukumar bazata lamunci hakan ya cigaba da faruwa a fadin Jahar Kano ba.
Kawo ya wannan lokaci Hukumar na cigaba da rike kayan inda take dakon shawarar lauyoyinta domin daukar mataki na gaba.
A karshe Garun Babba ya gargadi masu sana’ar buga takardu dasu shiga taytayinsu domin gujewa fushin doka. Ya kuma kara yin kira ga al’ummar Jahar Kano tare da jami’an tsaro da su cigaba da bawa Hukumar cikakken goyan baya da hadin Kai ta yadda za’a kawo karshen irin wannan aiyukan a fadin Jahar Kano.