Daga Zaharadden Sale
Samar da kungiyoyin mata, abune da zai karfafa ci gaban al’umma la’akari da irin gudummarwar da suke bayarwa tun daga tushe,
Shugaban karamar hukumar Dawakin Kudu Alhaji Sani Ahmad Mairago ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da sabuwar kungiyar kwarya tabi kwarya da akayi a garin Tamburawa, a karamar hukumar Dawakin Kudu.
Mairago Wanda kansilan mazabar Tamburawa Alhaji Garba Auwal ya wakilta, ya Yabawa shugabannin kungiyar bisa tunani da hangen nesa na Samar da kungiyar a wannan lokaci, inda yace karamar hukumar zata hada hannu da kungiyar wajen ayyukan cigaba a yankin.

A jawabinta Shugabar kungiyar Hajiya Salma Alhaji Gambo ta bayyana manufofin kungiyar da suka hadar da hada kan mata Dan taimakawa juna a fanin ilimi , kiwon lafiya da tallafawa cigaban kananan yara a garin Tamburawa da kewaye
Yadda Mijina ya sake ni bayan ya damfare ni – Mansura Isa
A nasa jawabin tsohon Dan majalisar tarayya na karamar hukumar Dawakin Kudu Mustafa Bala Dawaki Maigidan Ruwa Wanda tsohon Dan majalisa Jiha Muazzam El Yakub ya wakilta, ya Yabawa kungiyar bisa managartan tsatsare da bijiro dasu tare da yin alkawarin aiki kafada da kafada da kungiyar Dan Samar da Kyakkyawan Yanayi a fanin ilimin da sana’a.
Da yake jawabi Uban kungiyar Kuma dagacin garin Tamburawa Alhaji Auwalu Dantube yabawa shugabannin kungiyar yayi bisa jajircewar su na ganin kungiyar ta kafu abin dayace Hakan wata alamace ta samun nasara, daganan sai ya godewa daukacin bakin da suka halarci taron Kuma suka bada gudummmawar kudade da littattafai dan karfafawa kungiyar,